Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shirin Harajin Internet Da Gwamnatin Tarayya Ta Bullo Dashi

IMG 20240307 WA0056

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin dakatar da Babban Bankin na CBN da gaggawar dakatar da aiwatar da harajin ta yanar gizo da babban bankin ya kaddamar, kamar yadda dokar ta tanada. Majalisar ta nuna damuwarta kan yadda ‘yan Najeriya zasu iya fahimtar harajin da babban bankin ya fitar, domin bai yi daidai da ka’idojin da ke kunshe a cikin sashe na 44 (2a) na dokar aikata laifuka ta yanar gizo ba dangane da masu karbar harajin. A martanin…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Za A Kaddamar Da Shirin Hadakar Makarantu Kan Batun Tsaro

IMG 20240310 WA0186

Gwamnatin Jihar Kaduna zata hade wasu makarantun Sakandare dana firamare wajen guda da yawan su ya kai 359 dake yankunan da matsalar tsaro ta fi Kazanta a fadin Jihar. Manufar hakan shi ne tabbatar da cewar ko wane Yaro ya sami damar zuwa makaranta don samin ilimin daya da ce duk da kalubalen tsaro. Gwamnatin Jihar ta dauki wannan matakin ne bayan data sami rahoton raguwar alkaluman adadin Yaran da suke zuwa makaranta, saboda barazanar tsaro. Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani ne yake bayyana haka ta bakin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin…

Cigaba Da Karantawa

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Hukuncin Kisa Ga Masu Safarar Kwayoyi

IMG 20240310 WA0183

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar da ya bukaci hukuncin kisa kan masu safarar miyagun kwayoyi a kasar. Wannan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitocin da ke kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam, dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar. Shugaban kwamitin shari’a da ‘yancin dan adam, Sanata Mohammed Monguno daga jihar Borno ta Arewa, shine ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar Alhamis. Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na uku, na da nufin sabunta dokar haramta amfani da magunguna masu…

Cigaba Da Karantawa

Baragurbin Ministoci Ne Suka Sa Ba A Ganin Kokarin Tinubu – Sanata Ibrahim

IMG 20240510 WA0026

Yawancin ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa ba sa kokari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a jam’iyyar APC. Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu Yan Dagaji ne kuma ba sa tabuka komai. Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels. A cewar dan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin kasar, amma babu wani tsari da mataimaka…

Cigaba Da Karantawa

Badakalar Biliyan 2.7: Kotu Ta Bada Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa

IMG 20240509 WA0056

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, a zamain mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika da ‘yarsa Fatima kan naira miliyan 100 kowannen su. A ran Alhamis ne aka gurfanar da Sirika da ƴarsa a gaban kotun. Hukumar EFCC ce ta maka tsohon ministan a kotu domin a kwato wasu Naira biliyan 2.7 da take zargin an tafka harkalla a kansu lokacin yana minista. Sirika ya yi shekara takwas ya na Ministan sufuri sannan an gurfanar da shi tare da ‘yarsa Fatima,…

Cigaba Da Karantawa

SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Amfani Da Karfin Iko Wajen Hana CBN Amfani Da Harajin Internet

IMG 20240228 WA0023

Kungiyar Rajin Kare Haƙƙin Jama’a ta SERAP, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu cewa , “ya yi amfani da ƙarfin ikon sa ya gaggauta taka wa Babban Bankin Najeriya (CBN) burki, kada ya bari bankuna su fara cirar Harajin Daƙile Harƙallar Kuɗaɗe ta Hanyar Intanet, wato ‘Cybersecurity’ da aka ƙaƙaba cikin wannan satin. SERAP ta ce ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya biyan harajin ta hanyar cire masu harajin daga kuɗaɗen taransifa a bankuna, da Gwamnan CBN Yemi Cardoso zai fara, ya karya Dokar Najeriya ta 1999 da aka yi…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Najeriya Miliyan 32 Za Su Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Watan Yunin Bana

A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance. Akwai yiyuwar cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 ne zasu fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustar shekarar da muke ciki matukar ba’a dauki matakan gaggawa ba, a cewar rahoton Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda kwamitin kai dauki na kasa da kasa da gwamman…

Cigaba Da Karantawa