An Nada Shugaban Asusun Ba Wa Dalibai Bashin Kudin Karatu

IMG 20240427 WA0072

Shugaban ?asa Bola Tinubu ya amince da na?in Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ?alibai bashin karatu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da ya?inin mista Ovia zai yi amfani da ?warewarsa ta aiki wajen ganin ?aliban ?asar sun samu damar fa?a?a karatu ta hanyar samun bashi daga shirin da gwamnatinsa ta ?ullo da shi.

Mista Ovia – wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, kuma ?an kasuwa – na da digiri na biyu a fannin kasuwanci daga kwalejin kasuwanci ta Harvard da ke Amurka.

Bai wa ?alibai bashin karatu wani shiri ne da gwamnatin ?asar ta ?ullo da shi, don bai wa ?alibai damar yin karatu a manyan makarantun ?asar tare da samun cikakkiyar ?warewa, musamman tsakanin matasan ?asar.

Shugaba Tinubu ya yi fatan cewa mista Ovia zai gudanar da ayyukansa don tabbatar da cewa ?aliban ?asar sun samu ?warewar da suke bu?ata, a duka fannonin ilimi.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin ?asar ta ?ullo da shirin kafa asusun bai wa ?aliban ?asar bashi don ci gaba da karatunsu, a wani mataki na sau?a?a wa ?alibai ra?a?in ?arin ku?in makaranta da jami’o’in ?asar suka yi.

Related posts

Leave a Comment