Hukumar tattara kuɗin shiga a jihar Kaduna ta rufe rassa shida na bankin UBA saboda zargin kaucewa biyan harajin naira miliyan 14. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai samamen ne bayan da hukumar gudanar bankin ta gaza mutunta takardun da aka aike masu. Tawagar hukumar, bisa jagorancin sakataren hukumar gudanarwa da mai bai wa hukumar shawara kan shari’a, Barista Aysha Muhammad, ta rufe rassan bankin tare da tallafin jami’an tsaro. Barista Aysha ta ce “bisa sashe na 104 na dokar haraji, hukumar ta samu izinin kotu ta ƙwace tare da…
Cigaba Da KarantawaDay: April 25, 2024
Tsananin Zafi Ya Hallaka Sama Da Mutum 40 A Jihar Kano
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa hukumomia jihar sun fitar da wasu jerin shawarwari ga al’umma kan yadda za su kare kansu daga yanayin da ake ciki na tsanani zafi. Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton ƙaruwar zazzaɓi mai zafi da hukumomin lafiya a jihar suka danganta da ƙaruwar yanayin da kaɗawar busasshiyar iska. Bayanai na cewa irin wannan yanayi da aka shiga ya haifar da mutuwar mutum fiye da 40 sannan da dama suna cikin mawuyacin hali. Kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf…
Cigaba Da KarantawaDakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno
Dakarun Sojin Najeriya sun ce sun yi wa maɓoyar ‘yan ta’adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ƙananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno. Wata sanarwa da mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa ‘yan ta’ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu. Samamen na haɗin gwiwa tsakanin rundunar Operation Haɗin Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin ‘yan ta’ddan abin da ya tilasta wa da dama tserewa. Sai dai Gabkwet ya…
Cigaba Da KarantawaGwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Jirgin Sama Na Dana
Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana. Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed da ke Legas. Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin. Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin umarnin ƙa’idojin tafiyar da harkar sufurin jirage. Acikin wata…
Cigaba Da KarantawaShugaban Kasa Ya Kaddamar Da Tsarin Karbar Bashin Kayayyaki Ga ‘Yan Najeriya
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar. Tsarin zai bai wa al’umma damar inganta rayuwarsu ta hanyar samun bashin kayyaki inda za su riƙa biya sannu a hankali tsawon lokaci. Da tsarin, jama’a na iya sayen gidaje da motoci da samun ilimi da kiwon lafiya ta hanyar bashi, inda za…
Cigaba Da Karantawa