Zargin Nuna Wariya: Mun Ba Ministan Abuja Mako Biyu Ya Gyara Kurakuransa- Kungiyar Fararen Hula

images (25)

Gamayyar kungiyoyin fararen hula na Arewacin Najeriya tare da hadin gwaiwar kungiyar dake kishin Arewa wato, Northern Patriotic Front a turance, sun baiwa Ministan Abuja Barasta Nyson Wike makonnin biyu domin ya gyara zargin da su kayi masa na nuna wariya a jagorancin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya danka masa Amana a matsayin Ministan Abuja.

Jagoran kungiyoyin, Wanda jigo ne a jam’iyyar APC kana tsohon dantakarar Shugabancin Najeriya Kwamared Ali Abacha ne ya bayyana haka ga wakilimu a safiyar Alhamis din nan a garin Kaduna.

A cewar Abacha ” mun kudiri aniyar yin Taron manema labarai a Arewa House dake nan Kaduna, Amma Dattawan kungiyoyin mu wadanda Suma jagorori ne a Arewa sun kira mu inda suka bukace da mu mayar da wukarmu cikin kube” Amma fa Ina tabbatar maku da cewa Nan da sati biyu, muddun ba mu gani a kasa ba, to zamu dawo kan wannan matsayi.

Alal misali, kamar kama karya da shi Wike yayi na karbe kwantiragin kula da dakin taro na kasa da kasa dake Abuja, daga kamfanin intergreted facility management, mallakin Daya daga cikin jagororin mu, Kuma Dan jam’iyyar APC da ya sadaukar da Kansa a zabukan da suka gabata Sanata Abubakar Ahmed Mo’Alliyidi, wannan lamari, Sam bai mana dadi ba, Kuma Muna bukatar ganin Wike ya sauya matsayin da ya dauka a Kai.
A karshe Muna Mika jinjina ta musamman ga Shugaban kasa Bola Tinubu bisa matakan da yake dauka wajen farfado da darajar Naira domin inganta tattalin arzikin kasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply