Asusun Bada Lamuni Na Duniya (IMF) Ya Soki Lamirin Tinubu Na Dawo Da Tallafin Mai A Boye

IMG 20240226 WA0252

Asusun ba da lamuni da duniya (IMF) ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye. Hukumar ta ce dawo da tallafin da aka yi a boye zai cinye kusan rabin kudin shiga da kasar za ta samu daga arzikin man fetur.

Asarar da Najeriya za ta yi IMF ta ce matakin zai laƙume akalla N8.43trn daga cikin N17.7 trn da ake sa ran samu daga cire tallafin man fetur.

Wannan na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan Najeriya game da tallafin man fetur.

IMF ta ce taso a shafe maganar tallafin mai gaba daya a Najeriya cikin shekaru biyu kacal yayin da gwamnati ke kokarin kawo wasu shirye-shirye.

Najeriya ta na shigo da gas kasar Sai dai duk da yawan fitar da mai da Najeriya ke yi, ta na shigo da mafi yawan gas kasar saboda ba ta da matattun mai da za su wadaci ‘yan ƙasar.

A wani bangaren, Bankin Amurka ya ce Najeriya za ta rasa N7bn zuwa N10bn idan ta bukaci shigo da litar 18 zuwa 25 na gas.

Wannan martani na hukumar na zuwa ne kusan shekara guda bayan Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a kasar. Shugaban ya sanar da hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun bara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply