Sanata Ali Ndume ya soki harajin yanar gizo da babban bankin Najeriya ya bullo da shi kwanan nan, inda ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da dorawa ‘yan Najeriya haraji ba tare da kara musu kudaden shiga ba.
Dan majalisar Dattawa na jam’iyyar All Progressives Congress mai wakiltar mazabar Borno ta kudu ya bayyana haka a shirin Siyasar Yau na Channels Television a Jiya Juma’a.
Ndume ya jaddada cewa harajin da aka saka ta yanar gizo zai kara dora wa ‘yan Najeriya nauyi, Yana mai cewa, “Ba za ku iya ci gaba da dora wa mutane haraji ba tare da inganta kudaden shiga ba. Idan ba a faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga Bai kamata Ku sanya musu haraji ba.
A ranar 6 ga watan Mayu ne CBN ya fitar da wata takardar da ke ba bankunan ajiya ajiya, masu gudanar da hada-hadar kudi ta wayar salula, da masu ba da sabis na biyan kudi da su fara cire harajin da za a tura wa asusun ajiyar yanar gizo na kasa, wanda ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ke gudanarwa. Shirin karbar harajin ya fuskanci tofin Allah tsine, inda kungiyoyin kwadago ke barazanar daukar mataki a duk fadin kasar idan gwamnati ba ta sake Kudirin ba.