Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa Zazzabin Lassa ta yi ajalin mutum 156 sannan mutum 857 sun kamuwa da ita daga Janairu zuwa ranar 28 ga Afrilu 2024.
Hukumar ta ce alkaluman yaduwar cutar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a wannan lokaci ya zarce yawan mutanen da cutar ta kashe a irin wannan lokacin shekarar 2023.
NCDC ta ce an samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar daga mutum 11 a mako 16 zuwa mutum 14 a mako 17.
An samu karuwa a yawan mutanen da ake zargin sun kamuwa da cutar daga mutum 5084 a 2023 zuwa 5963 a 2024.
Rahoton ya nuna cewa kashi 63% daga cikin mutanen da suka kamu da cutar an gano su ne daga jihohin Ondo, Edo da Bauchi sannan kashi 37% daga jihohi 25.
Cutar ya fi kama mutane masu shekaru 21 zuwa 30.
Hukumar ta gano cewa rashin zuwa asibiti a lokacin da ya kamata, rashin sani da rashin tsaftace muhalli na daga cikin matsalolin dake yada cutar.
Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da zazzabin lassa
Tsaftace muhalli: A Rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wurare.
Zubar da shara: Idan aka Tara shara kada a rika zubar da shi kusa da gida a rika kaiwa can waje.
Killace Abinci da ruwan Sha: Yin haka zai taimaka wajen hana bere ko kwari shiga cikin abinci ko ruwan sha.
Dafa nama: Kafin a dafa nama kamata ya yi a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Tsafta: A yawaita wanke hanaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci a inci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake Koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyauewa waje. Kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
Wanke gawa a cikin daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ko Kuma a inda ya kamata.