Ilimin ‘Ya’ya Mata Shi Ne Tubalin Ginin Al’umma – Alawiyyah Aminu Dantata

An bayyana ilimin ‘ya’ya Mata a matsayin wani tubali wanda ke gina al’umma gaba daya kasancewar duk wanda ya ba ‘ya mace ilimi to tamkar ya ba al’umma gaba daya ne.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar makarantar Nurul Huda Islamic Academy dake Kaduna Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin yayen daliban makarantar wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna.

Ta ƙara da cewar a tsarin da suka ɗauka a makarantar Nurul Huda shine bada ilimi daga matakin farko na Firamare domin muddin aka inganta ilimi daga tushe babu shakka a dauko turba na bunƙasa ilimi.

Daga karshe Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata ta bukaci iyaye su tashi tsaye wajen ba ‘ya’yan su Ingantaccen Ilimi domin babu wata gata da za ka bar wa zuriyarka illa ka basu ilimi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply