Shugaban kungiyar shugabannin kananan Hukumomin Jihar Kaduna Honorabul Shu’aibu Bawa Jaja yace kungiyar tasu na iyaka bakin kokarinta wajen ganin an daidaita ?angaren majalisa da wasu shugabannin kananan hukumomi 3 da majalisar ta dakatar.
Bawa Jaja ya sanar da hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a ofishin sa dake ma’aikatar kula da ?ananan hukumomi dake Kaduna.
Shugaban kungiyar ya ?ara da cewar dukkanin shirye shirye da matakan da ya kamata a ?auka sun yi nisa wajen shawo kan matsalar wanda ya bayyana shi a matsayin na rashin fahimta.
Daga karshe Bawa Jaja ya bada tabbaci ga jama’ar Kaduna cewa a matsayin su na shugabannin kananan hukumomi za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.