Abin mamaki ne yadda ‘yan siyasa masu i?irarin addini da kare martabar almajirai suke shiga rigar almajirci suna fakewa da addini don cinma wata bukatar su ta siyasa da son zuciya.
Mun wayi gari da ganin wasu rubuce rubuce dake korafi akan saka mai girma tsohon gwamnan mu na jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El rufai a jerin wadan za’a tantance a matsayin minista daga jihar Kaduna kuma ake danganta wannan labarin da gidan daya daga cikin manyan Malaman da ake girmamawa a kasar nan.
Har ga Allah babu wanda yake shakka akan cewa Malam Nasiru El rufai ya cancanci ya rike kowane irin mukami a wannan kasa tamu wanda irin su aka rasa ya sa mu cikin halin da muke ciki a wannan kasar, ai ko wanda baya son Malam Nasiru idan zai yi adalci ya fadi gaskiya ya san Malam Nasiru Ma’aikaci ne na gaske da kasa zata amfana da kwarewar sa da jajircewar sa, kuma shi wannan mai magana ya sani ?ur’ani ya fada mana cewa kada kiyayyar wasu Jama’a ya hana kuyi masu Adalci kuma a harkar mulki abinda Qur’ani ya nuna mana shine a ba amintacce wanda zai iya ba wanda kake so ba ko wanda ya ke baka wani abun duniya ba.
Mun tabbata Malam Nasiru El rufai yayi iyaka kokarin sa wajan kwatanta adalci a jihar Kaduna bai yarda da danniya ko zalunci ba shi yasa wasu daga abokan zaman mu na kudancin Kaduna ba sa so ma suji an ambaci sunan sa wannan ya sa ma har muke ganin ko ana so ayi amfani da wasu daga cikin mu ne domin a bata sunan Malam din da sunan Almajirai
Muna kira da Jama’a da idan za suyi siyasa su fito fili kawai a goga da su ba laifi bane amma su daina fakewa da addinin domin musulunci bai yarda da ci da addini ba!
Mun sani lokacin zabe kun fito fili kun nuna baku tare da mai girma shugaban kasar nan namu na yanzu Bola Ahmed Tinubu babu yadda bakuyi ba akan kar a zabe shi amma daya ke mulki na Allah ne Allah ya bashi hatta wadan da suke da alaka ta almajirci da ku basu bi ra’ayin ku ba sunyi abinda ya fisshe mu na zaben Uba Sani a jihar Kaduna da kuma Bola Tinubu a tarayyar Najeriya.
Mun san irin kulle kullen da kukeyi ku ga kotu ta wargaza wannan zaben domin a dora wanda ku ke so amma ta Allah ba taku ba kuma Allah yana bayan mai gaskiya kuma mai kyakkyawar zuciya.