Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Jigon jami’yyar PDP, Segun Showunmi ya magantu kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya yaudari na hannun damansa. Showunmi ya nuna takaici musamman kan yadda shugaban ya ci amanar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello duk da wahalar da suka sha masa.
Jigon PDP ya bayyana haka a shafinsa na X inda ya ce da saka hannun Tinubu a dukkan matsalolin da tsoffin gwamnonin biyu ke ciki.
Ya ce zai yi wahala Majalisar Dattawa ta ƙi tantance El-Rufai a matsayin Minista idan da Tinubu ya shiga lamarin.
“Yarbawa sun dauki cin amana akansu kamar yadda ake cewa muna amfani da mutum idan muka samu biyan buƙata kuma mu watsar dashi.” –
Segun Showunmi Ya ce El-Rufai da Bello sun bautu “Kamar Tinubu bai damu da abubuwan da za su faru ko za su biyo baya ba.” “Ku duba yanzu halin da El-Rufai ya ke ciki duk da irin goyon bayan da ya ba Shugaba Tinubu a zabe.”