Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bada Tallafin Karatu Ga Daliban Arewa

Gidauniyar tunawa da marigayi Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta ba da tallafin karatu ga dalibai 200 wadanda suka fito daga jihohi 19 na Arewa har da Abuja.

Shugaban Gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar ya sanar da hakan a tattaunawar shi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala bikin bayar da tallafin wanda ya gudana a Kaduna.

Injiniya Gambo ya ƙara da cewar tallafin karatun kebe shi ne kawai ga dalibai dake karantar ɓangaren kimiyya da fasaha a manyan makarantun Najeriya.

“Mun zaɓo dalibai guda goma goma daga jihohi 19 da Abuja inda ya kama jiha 20 kenan, kuma tallafin mun ware shi ne kawai ga dalibai masu hazaƙa waɗanda ke fuskantar kalubale wajen biyan kuɗaɗen makaranta.

“Kuma mun tabbatar da cewa daliban da suka ci gajiyar sun kasance wadanda suke da akalla CGB 2.5 zuwa sama a jami’o’i da Kwalejojin kimiyya da fasaha.

“Muna matuƙar farin ciki da yadda ƙoƙarin namu ya taba wadanda ake bukata wato ‘ya’yan talakawa kamar yadda mai girma marigayi Sardaunan Sokoto ya yi aniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply