Fiye Da Yara Miliyan Guda Ke Mutuwa Duk Shekara A Najeriya – Ministan Lafiya

images 2024 03 12T063814.559

Ministan Lafiya a Najeriya, Farfesa Ali Muhammad Pate ya ce kimanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar na mutuwa duk shekara sakamakon cututtuka ciki har da waɗanda rigakafi ke samar da kariya daga kamuwa da su.

Ministan ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce kashi 70 cikin 100 na mace-macen ana iya kare su.

“Bari mu yi bayani, akwai kimanin mace-macen yara miliyan ƴan ƙasa da shekara biyar duk shekara a ƙasar nan, kashi 70 na mace-macen sakamakon cututtuka kamar mashaƙo da ƙyanda da nimoniya da ake iya kandagarkinsu ta hanyar yin rigakafi da kuma sauran rigakafi da ake da su wadanda ba su da tsada.

Farfesa Pate ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ta bijiro da tsare-tsare da za su shafi rayuwar talaka inda ya ce zuba hannun jari a ɓangaren lafiya na daga cikinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply