Babu Cushen Da Aka Yi Cikin Kasafin Kudin Bana – Gwamnatin Tarayya

IMG 20240225 WA0030

Fadar Shugaban kasa ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda Shugaban kasar ya sanyawa hannu a watan Janairu.

Ɓangaren zartarwar ta mayar da martani ne kan wata hira da BBC ta yi da shugaban ƙungiyar ƴanmajalisar dattawan ƙasar na yankin arewa, Sanata Abdul Ningi wanda ya yi zargin cewa kasafin kuɗin da bangaren zartarwa ke aiki da shi ba shi ne majalisun dokokin kasar suka rattabawa hannu ba.

Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ba kamshin gaskiya a zargin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply