Tsaro: Ya Zama Wajibi Gwamnatin Kaduna Ta Sauya Salo – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman wanda akafi sani da Mr LA ya bayyana rashin gamsuwarsa da irin rikon da gwamnatin jihar Kaduna takewa sha’anin tsaron jihar. Mr LA yayi wannan bayani ne biyo bayan samun labarai da dama kan yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a fadin jihar kaduna.

Ko a ranar lahadi yan bindiga sun shiga har cikin makarantar Nuhu Bamalli dake zariya inda sukayi awon gaba da malamin makarantar da wasu daga cikin iyalan sa. Sannan ko a jiya yan ta’addan sun kara kafa shinge a hanyar Abuja zuwa kaduna sukai garkuwa da mutane tare da kashe wasu mutane 2. Duk da gwamnatin jihar ta bayyana cewar ta amso mutane tara daga cikin Wanda akai garkuwa dasu.

Ya zama wajibi gwamnatin jihar ta dauki sabbin dubaru wurin fuskantar matsalolin tsaron da suka addabi jihar kaduna, sannan ya zama wajibi mutanen gari suma su taimakawa jami’an tsaro da muhimman bayanan sirri Wanda zai dinga taimaka wa wurin dakile ire iren wa’innan hare – hare.

Kusan kowani manyan hanyoyin jihar kaduna babu tsaro a halin da muke ciki, domin hanyar birnin gwari bata biyuwa, hanyar Abuja zuwa kaduna shima kusan kullum saikaji anyi garkuwa da mutane, yanzu kuma hanyar zariya ita ma anzo har cikin makaranta. Wannan ba karamar barazana bace ga daliban mu mata da maza dake karatu a wannan makarantar musamman ganin cewar yanzu ne daliban suka fara dawowa tun bayan dogon hutun da sukayi sakamakon bullar cutar covid 19.

Daga karshe ‘dan takarar Sanatan a karkashin jam’iyyar PDP hon Lawal Adamu Usman Mr LA yayi addu’ar samun saukin wannan matsalar ta tsaro data addabi yankin arewa tare da janyo hankulan shuwagabanni dasu sani cewar sunyi rantsuwar kare dukiya da ran mutanen jihar su lokacin zabe dan haka su sani Allah zai tanbaye su akan nauyin da ya rataya a kawunan su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply