Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce wajibi sun tinkarin wannan aiki tare domin kaucewa tufka da warwar.
“Ina jin yaki da batun rashin bai daya zai taimaka, saboda idan muka kora ‘yan bindiga zasu koma jihar Zamfara amma idan a can Zamfara ana daukar irin wannan mataki lokaci guda can ma za a turo su, to da haka zamu magance lamarin baki daya”, inji Radda.
A nasa jawabi, gwamnan jihar Zanfara Dauda Lawal wanda shima ya yi ra’ayi da gwamnan Katsina ya ce “idan muka yi kokarin magance wannan matsala zai taimaka wurin shawo kan manyan matsalolin dake addaban al’ummar mu, abin fari ciki shine zamu yi wannan aiki tare.
Duk da cewar jihohin arewa na fama da matsaloli musamman maso yamma, akwai jihohi kamar su Filato da Neja da Benue dake arewa maso tsakiya da gwamnoninsu suka halarci taron kuma suka bayyana irin matsaloli da suke fuskanta.
Gwamna Caleb Mftwang na Filato ya ce dole ne a tantance yanayin kowace jiha domin sanin yanda za a tinkari matsala ta kowace jiha kuma ya ce arewa ta tsakiya ta dade tana fama da matsalar tsaro kafin yankin yamma ta biyo sawu.
Ya ce “idan muka nemi shawo kan lamarin da salo iri guda ba zamu samu sakamakon da muke bukata ba, ya kamata a tantance sosai kuma a duba yadda kowace al’umma take, haka zai sa mu fahimci matsalolin su da kuma hanyar magance su.
Uba Sani na Kaduna ya kyautata zaton yin hadin kai da wannan cibiya zai taimaka da yaki da ta’addanci a Najeriya
Cibiyar, wadda ta shahara wurin tallafawa shirye-shiryen zaman lafiya a duniya, ta ba gwamnonin damar bayyana irin kalubalolin da suke fuskanta domin neman hanyoyin magance matsalolin tsaro a yankin.