Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, talatin ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Nuwamba na shekarar 2020.

  1. Ministar jinkai Sadiya, da ta al’amuran mata Tallen sun raba wa mata su dubu dari da hamsin, naira dubu ashrin kowacce, tallafi na sana’a na Gwamnatin Tarayya a jihar Bauci.
  2. Ana ci gaba da horas da sabbin ‘yan sanda kurata na musamman (Special Constable) a jihohi daban-daban na kasar nan, har a jiya aka gama horas da sabbin kuratan su dari takwas da saba’in da bakwa a jihar Edo, a jihar Imo kuwa su dari hudu. Har Obaseki ya fara ba na jiharsa aikin su danko masa fursunonin da suka tsere a lokacin zanga-zangar da aka yi.
  3. Kidinafas, sun je harabar kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke UPE a hanyar Zariya, shekaranjiya wuraren karfe tara na dare, suka tafi da malami daya, da yara biyu, suka kuma harbi wani da ya tsere, yana asibiti yana jinya.
    Haka nan kidinafas sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja jiya, daidai Katari, suka harbi na harbi, suka yi kidinafin na kidinafin.
    Haka nan ba a dade ba da kidinafas suka je Rigachikun ta jihar Kaduna, suka kashe mai juna biyu, suka tafi da mijinta. Haka nan ba a dade ba wasu ‘yan bindiga suke je yankin Ikara ta jihar Kaduna suka kashe wani mai gari. Haka nan ba a dade ba, makasa suka je Kidandan ta yankin Giwa ta jihar Kaduna, suka kashe mutane rututu, kuma har yau ba su kyale mutanen yankin sun sakata ba. Haka nan kidinafas na nan sun hana bin hanyar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, haka nan suna kokarin kwace hanyar Kaduna zuwa Zariya. mutanen yankin Zariya sabon Garin Zariya, da Zangon da ke kusa da Samarun Zariya, har da na gidajen jami’ar A.B.U duk da ke jihar Kaduna, ba su tsira daga kidinafas, da barayin shanu, da makasa ba. Haka ma yankin Mando da ke cikin garin Kaduna, kidinafas na kai musu ziyara. Na Mahuta da ke kusa da asibitin ido na Kaduna su ma ba sa iya rintsawa sosai. Haka nan yankin Kasuwar Magani, da ke jihar Kaduna, kidinafas na musu dauki dai-dai da kisan mummuke.
  4. A yankin Dan Musa da Batsari na jihar Katsina, ‘yan sanda sun damke wasu ‘yan bindiga su goma sha biyar, da shanu da sauran dabbobi masu tarin yawa.
  5. Sojoji sun dakile wasu hare-hare da ‘yan Boko Haram suka kai, har da na ‘yan ISWAP, suka damke wani mai kera musu bam a Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
  6. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da a kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu, sun cika shekara biyu ke nan, suna dakon ariyas na sabon albashi.
  8. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos, mutum 152 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 136
Kano 4
Neja 3
Ekiti 2
Kaduna 2
Ogun 2
Taraba 2
Abuja 1

Jimillar da suka harbu 65,148
Jimillar da suka warke 61,078
Jimillar da ke jinya 2,907
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,163

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina shawagi a fesbuk, sai na yi kibicis da rubutun da Farooq Kperogi, wani babban lakcara dan Nijeriya, da ke zaune a Amurka yana koyarwa ya yi kamar haka:

From Farooq Kperogi

With the current hike of petrol price in Nigeria to N170 per liter (which adds up to N680 per gallon), it means Nigerians are now paying $1.79 per gallon of petrol (using an exchange rate of N380.5 to a dollar).

Well, I just bought petrol here in the Atlanta area at $1.62 per gallon. To paraphrase Buhari, it makes no sense for petrol to be cheaper in the US, the world’s wealthiest country, than in Nigeria, the world’s poverty capital.

Na yi nan.

Yau ladanan karfe hudu daidai suka soma rige-rigen kiran assalatu. Ban dai ji zakara ko daya yana cara ba ko an yi farfesunsu ne?

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply