Fafaroma Francis ya ce yana buga wa cocin Katolika da ke Gaza waya kullum domin sanin halin da mutanen yankin ke ciki.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CBS, Fafaroma ya ce daruruwan Falasdinawa da ke gudun hijira na fama da rashin abinci.
Fafaroma ya ce a lokacin da aka kashe Uwa da ƴarta a harabar cocin, rikicin ya tashi daga yaƙi ya koma ta’addanci.
Manyan mutane da ƙungiyoyi da dama dai na sukar yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.