2023: Wasu Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Kudu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu daga cikin Gwamnonin APC a Arewa ba su yarda cewa sai ɗan takarar Arewa kaɗai zai iya kayar da Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP ba.

Aƙalla Gwamnoni 9 na APC daga Arewa na ta gaganiyar ganin cewa sauran gwamnoni sun amince a bai wa ɗan Kudu takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC, a zaɓen 2023.

APC dai ta na da gwamnoni 14 a Arewa, sannan kuma ta na da 8 a Kudu, kuma ɓangarorin biyu na ta kashe rana da dare su na taro a asirce, domin ganin an fitar da ɗan takara ɗaya tilo, kamar yadda Shugaba Buhari ke so a yi, ba tare da an gwabza wajen zaɓen fidda gwani ba.

A ranar 6 zuwa 8 Ga Yuni ne APC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, daga cikin mutum 23 da aka tantance.

Labarai Makamanta

Leave a Reply