Fina-Finai: Gwamnatin Kaduna Za Ta Gina Fim Village

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar babban sakataren hukumar KADIPA na jihar Kaduna, Khalil Nur Khalil ya cigaba da kokarin ganin an gina kauyen shirya wasan kwaikwayo wato’Fim Village’.

A wani jawabi da ya fito daga shafin KADIPA a dandalin Twitter a ranar Alhamis, an fahimci gwamnatin Kaduna tana nan a kan aikin ‘Film Village’ domin bunkasa rayuwar matasa.

Khalil Nur Khalil ya hadu da wakilan KCTA, shugabar Fasaha Café, Joseph Ike, da fitacciyar ‘yar wasar kwaikwayo, Rahma Sadau a kan wannan shirin. Shugaban na KADIPA ya yi wannan zama ne da nufin ganin yadda a za a iya gina kauyen shirya wasan kwaikwayo da zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, aikin zai taimaka wajen kafa Kaduna Film Village a hukumance domin sa ido a kan harkokin wasan kwaikwayo a Kaduna. Haka zalika ana neman gina wannan kauye a filin kasuwar baje-kolin Duniya a Rigachikun, ana sa rai wannan zai jawo kwarararrun ‘yan wasan kwaikwayo.

Akwai taurari a garuruwan Legas, Capetown, Accra da Dubai da za ayi amfani da su wajen horas da kananan yara masu tasowa domin su kware a harkar fim. Wani aiki da KADIPA ta ke son yi shi ne shirya bikin wasan ‘yan fim da marubutan wasan kwaikwayo na gida domin su hada-kai da na taurarin Duniya.

A karshe kuma shugaban hukumar zai tallata wannan aiki da nufin samun masu hannun jarin da za su narka dukiyarsu domin a kirkiri dinbin ayyukan yi a jihar. Muddin aka ci nasara wajen wannan aiki, matasa da-dama za su samu abin yi, su daina zaman banza.

Shekarun baya gwamnatin tarayya ta taba kawo shawarar yin irin wannan aiki a jihar Kano, amma wasu su ka nuna cewa hakan zai iya jawo lalacewar tarbiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply