Ƙetare: Shugaban Kasar Tanzaniya Ya Mutu

Rahotanni daga ƙasar Tanzaniya na bayyana cewar Shugaban kasar John Pombe Magafuli ya mutu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa ‘yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar domin nuna juyayi.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a wani asibiti dake babban birnin ƙasar Dar es Salaam.

An shafe makwanni ba a gansa a fili ba hakan ya tilastawa ‘yan adawa da sauran jama’ar kasar fara tambaya a game da shi.

Marigayin, mai shekaru 61 ya rasu ne bayan makwanni da aka zargi ya kamu da kwayar cutar korona mai kisa.

Magafuli bai amince a rufe makarantu, ma’aikatu da sauran harkoki ba kamar yadda aka yi a wasu kasashe inda ya ce mutane su koma masallatai da coci-coci su yi addu’o’i domin cutar ba za ta samu duk wanda ya rungumi addua ba.

Hakazalika, bai gamsu da ingancin rigakafin annobar ta korona ba don haka ya ce gwamnatinsa ba ta da wani tsari na siyan alluran rigakafin.

“Mu yan Tanzania ba zamu rufe kan mu ba, kuma ba zan sanar da ko rana guda na zaman gida ba domin Ubangijin mu rayayye ne, kuma zai cigaba da kare mu a Tanzania,” kamar yadda marigayin shugaban ya shaidawa jama’a.

An haife shi a ranar 29 ga watan Oktoban 1959, ya girma a wani kaye da ke arewa maso yammacin yankin Chato da ke kusa da Tafkin Victoria.

Labarai Makamanta

Leave a Reply