Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a ranar da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ƴancin kai.
Wannan ne jawabin Shugaba Buhari na ƙarshe a irin wannan rana ta samun ƴancin kai a matsayinsa na shugaban ƙasar Najeriya ganin cewa zai sauka a 2023.
Cikin abubuwan da ya yi magana a kai a yayin jawabin har da batun gudanar da sahihin zaɓe a 2023.
Ga dai wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya yi magana a kan su:
Haɓaka tattalin arziki, yaƙi da cin hanci da inganta tsaro
Cikin abubuwan da Shugaba Buhari ya yi magana a kansu a yayin jawabin da ya yi har da batun haɓaka tattalin arizikin Najeriya inda ya ce tun a lokacin da aka zaɓe shi, ya yi alƙawarin haɓaka tattalin arziƙi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma inganta tsaro.
Shugaban ya bayyana cewa daɗin daɗawa kan waɗannan alƙawuran, gwamnatinsa ta kuma sha alwashi da yin tsayuwar daka wajen ganin cewa ta cire Ƴan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekara goma.
Sai dai shugaban ya bayyana cewa da taimakon Ubangiji, gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari wurin cika waɗannan alƙawuran da goyon bayan ƴan ƙasar da dama amma duk da haka a cewarsa kwaliyya ba ta kammala biyan kuɗin sabulu ba.
Shugaban ya bayyana cewa ɗaya daga cikin wuraren da gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari shi ne bangaren yaƙi da cin hanci inda ya ce sakamakon inganta ɓangarorin yaƙi da cin hanci da kuma taimakon ƙasashen waje an mayar da kuɗaden haram masu yawa da aka sace aka fitar waje.
Ta ɓangaren tsaro kuma, shugaban ya bayyana cewa an yi ƙoƙari wajen rage rikicin da ake yi a arewa maso gabashin ƙasar, da rikicin ƴan tayar da ƙayar baya a yankin Neja Delta da kuma rikice-rikicen ƙabilanci a wasu sassa na Najeriya da sauran matsalolin da ke yi wa ƙasar barazana.
Haka kuma Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnatinsa sakamakon tsare-tsaren da ta yi amfani da su wurin fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga har sau biyu.
Inganta harkar noma
A yayin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta bai wa ɓangaren noma fifiko ta hanyar fito da ƙanana da matsakaitan shirye-shirye da suka samar da ayyuka ga miliyoyin mutane.
Shugaban ya kawo misali da shirye-shirye irin su Anchor Borrower wanda ya ce Ƴan Najeriya sun samu tagomashi ta bangaren samun wadataccen abinci da kuma jawo hankalinsu kan ɗaukar noma a matsayin sana’a.
Shugaban ya bayyana cewa fitar da kayayyaki da ƙasar ke yi musamman amfanin gona da sauran abubuwa na kimiyya da fasaha za su taimaka wa kasuwar hada-hadar kuɗi ta ƙasar.
Yajin aikin ASUU
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a yayin jawabin nasa ya bayyana cewa yana matuƙar baƙin ciki sakamakon cikas da ake samu akai-akai a ɓangaren ilimin gaba da sakandare a ƙasar.
“Ina kira ga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da ta koma aji kuma ina ba su tabbacin cewa zan share musu hawayensu da ɗan abin da muke da shi duk da muna rashin kuɗi,” in ji shi.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wurin magance matsalar wadda aka shafe shekara 11 ana fama da ita.
Shugaba Buhari ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙari wurin tattara kuɗi a ciki da wajen ƙasar domin tallafa wa ɓangaren ilimi don tabbatar da cewa ƴan ƙasar sun samu ingantaccen ilimi.
Gudanar da sahihin zaɓe a 2023
Kan batun zaɓe kuwa, Shugaba Buhari ya yi alƙawarin ƙara inganta harkar zaɓe a ƙasar a yayin da ake fuskantar zaɓen 2023 da ke tafe.
Shugaban ya bayyana cewa duk wani ci gaba da aka samu a ƙasar idan ba a zaɓi shugabanni ta ingantacciyar hanya ba duk wani ƙoƙari da aka yi ba zai isa ba.
Shugaban ya kawo misali da zaɓen da aka yi a kwanakin baya a Jihohin Anambra da Ekiti da Osun da wasu mazaɓun tarayya inda ya ce an yi zaɓen gaskiya da gaskiya.
Game da zaɓen 2023 da ke tafe, shugaban ya yi kira ga ƴan takara da su gudanar da yaƙin neman zabensu cikin lumana da kuma kiyayewa daga kalaman ɓatanci ga juna.
Haka kuma shugaban ya bayyana cewa yana sa ran za a samu ƙarin matasa da mata a zaɓen da za a gudanar da ke tafe.
Kiwon lafiya
Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari matuƙa wurin inganta ɓangaren kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa musamman idan aka yi duba da lokacin annobar korona, ƙasar ta taka rawar gani da har ya sa ƙasashen duniya suka jinjina mata.
Shugaban ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya da ta ba mara ɗa kunya ta hanyar juriya da mayar da hankali bayan duniya ta yi hashen cewa tana daga cikin ƙasashen da annobar korona za ta yi wa ɓarna