Zan Yi Mulki Na Adalci Idan Na Lashe Zabe – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga birnin Ibadan na Jihar Oyo na bayyana cewar a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ba yan Najeriya tabbacin cewa zai zamo mai gaskiya da adalci ga kowa.

Tinubu ya bayar da tabbacin ne yayin da yake jawabi a wani taro da shugabannin Musulunci daga kudu maso yamma a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ƙarshen mako.

Dan takarar na APC ya yaba ma shugabannin addini a kasar kan addu’o’i da suke ci gaba da yi a kasar, wanda ya taimaka wajen hadin kai da zaman lafiya da aka samu a tsakanin al’umma.

Da yake magana kan babban zabe mai zuwa, Tinubu ya bukaci malaman Musulunci da su ilimantar da mabiyansu kan muhimmancin sauke hakkin da ya rataya a wuyansu da zabar yan takarar da ke da tarihi mai kyau a aikin gwamnati.

“Wannan lokaci na zabe lokaci ne na dunkule gaskiya da karya. Ina son zaben ya kasance a kan turba ta gaskiya.”Menene tarihin kokarin dan takara kuma menene manufofinsa? Na nemi ku bukaci magoya bayanku da su fito sannan su yi zabe kuma su yi hakan cikin hikima. Ku zabi yan takara masu hangen nesa don ci gaba da zaman lafiya Najeriya ta yadda kundin tsarin mulkinmu da yancin doka zai kasance bisa juriya da tausayi.”

“Alkawarin da na dauka na yin gaskiya da adalci ya yi daidai da ka’idojin addinin Musulunci. “An bukaci Shugaba a irin wannan alkarya tamu ya zamo shugaba mai adalci ga kowa. Idan aka zabe ni, zan yi shugabanci cikin gaskiya da damokradiyya daidai da kudin tsarin mulkin kasarmu.”

Tinubu ya yi alkawarin amfani da wannan gogewar wajen jagorantar Najeriya don daukaka kasar da sabonta fatan yan Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply