Akwai Bambanci Mai Yawa Tsakanin Buharin Da Dana Yanzu – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki lamirin Shugaba Muhammadu Buhari akan harkar tsaron ƙasar nan, Obasanjo, ya ce, abin takaici ne yadda shugaban kasa mai matsayin babban hafsan hafsoshin kasar nan ya gaza kawo karshen ‘yan tayar da ƙayar baya.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi da masanin tarihin nan, Toyin Falola, inda ya buƙaci shugaban ƙasa mai ci da ya farka daga dogon baccin da yake yi, domin fuskantar matsalolin da ke addabar ƙasar.

Obasanjo ya nuna rashin yardarsa kan iƙirarin da wasu ke yi na cewa ba shugaba ƙasar ba ne ke juya kujerar mulkin ƙasar.

“Zan iya cewa na san Shugaba Buhari saboda ya yi aiki da ni. Amma sau da yawa na kan tambayi mutane, shi ne ko kuwa ya canza ne daga Buhari da na sani?.

Ban yarda da maganar wasu mutane na barkwanci da ke cewa wannan Buharin wai daga Sudan ya ke ba, duk da na san hakan shirme ne, amma tabbas Buhari ya sauya matuƙa daga yadda na san shi a lokacin da muka yi aiki a gidan Soja.

“Amma bisa abin da nake gani, na yi imani watakila zai yi tunani akan abin da ya gada. Wataƙila zai ɗau darasi daga abin dake faruwa ‘yan kwanakin nan.

Idan kai babban kwamanda ne ana samun tashe tashen hankula na faruwa, to ya kamata ka farka,” a cewarsa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply