Shugaban rundunar yan sandan Najeriya. Usman Alkali Baba ya yi zargin wasu gwamnoni ke daukan nauyin ‘yan daba da ke kai hare-hare yayin kamfen din abokan hamayyarsu domin haifar da rikici.
Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, yayin da ya ke magana da jam’iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta INEC da masu ruwa da tsaki a zaben 2023 a birnin tarayya Abuja.
Amma, Alkali-Baba bai ambaci sunayen gwamnonin ba yayin da ya ke bayyana cewa kawo yanzu an samu hare-haren siyasa 52 tun fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023.
Ya ce ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin magance matsalar da ke tasowa. Shugaban yan sandan ya kuma gargadi yan siyasa kan muggan abubuwa da ka iya kawo matsala a zaben na 2023.
Ya bayyana hatsarin da ke tattare da rikici a zaben shugaban kasa na 2023 IGP din ya kara da cewa a baya, tashin hankula yayin zabe ya kasance barazana ga cigaban demokradiyya.
“Wannan taron ya zama dole biyo bayan abin da ke neman zama ruwan dare a kasar, idan ba a magance shi cikin gaggawa ba zai iya rikidewa ya zama barazana ga tsaron kasa da ma zaben.”