Za Mu Kawar Da Mabarata A Titunan Kano – Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ?ar?ashin Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Umar Ganduje zata fara kwashe mabarata da masu tallace-tallace da kuma sauran mutanen da ke yawo a tititunan jihar suna takurawa mutane ba tare da wani dalili ba.

Kwamishiniyar mata ta jihar, Dr Zahra’u Muhammad ce ta sanar da haka ranar Litinin a Kano a zantawar da tayi da manema labarai.

Dr ta bayyana cewa tuni gwamnati ta tattauna da masu ruwa da tsaki ciki harda masu unguwanni da shugabannin addinai da kuma masauratun gargajiya guda biyar dake jihar don saukaka hanyar da za a bi wajen kawar da barace-barace a titunan jihar.

Saboda wannan aiki, gwamnati ta ware Naira miliyan hudu don gudanar da aikin a fadin jihar.

“Mun kammala shirye shirye don tsaftace tititunan Kano daga masu tallace-tallace da mabarata don tabbatar da tsafta da rage ayyukan ta’addanci a fadin tititunan.
“Za mu fara aikin daga ranar Laraba kuma zamu tabbatar da an tsaftace tititunan.”

Ma’aikatar kuma ta bayyana yadda ta karbi rukuni biyu na Almajirai daga Kaduna a baya bayan nan Akwai maza da mata 47 da ke fama da rashin muhalli wanda za a taimaka musu a kuma kawar da su daga tititunan Kano.

Related posts

Leave a Comment