Taɓarɓarewar Tsaro: Ba Mu Tsanmaci Haka A Wannan Gwamnatin Ba – Bauchi

“Halin da Najeriya ta tsinci kanta yanzu hali ne na tashin hankali da fita hayyaci wanda a baya ba’a taɓa gani ba, babu wani mahaluki a yanzu a kasar wanda yake cikin kwanciyar hankali, abubuwa sun taɓarɓare kowa na cikin tsoro mai razanarwa, lamarin da ya kai ga ‘yan ƙasa yanke tsanmani daga Gwamnati gaba ɗaya”

Kalaman mashahurin Malamin Ɗarikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi kenan, lokacin da yake tsokaci dangane da halin taɓarɓarewar tsaro dake cigaba da addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar a karkarshin jagorancin mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Babban malamin yace hakkin gwamnati ne ta kare ‘yan kasa daga ‘yan bindiga da sauran miyagun da suka addabesu, nauyi ne wanda ke kan kafaɗun Gwamnati na kare dukiya da rayukan ‘yan Najeriya waɗanda rayukansu ke cikin hatsari sakamakon fitinar ‘yan Bindiga.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan tsokacin ne bayan karbar wakilan Kiristoci da yayi wanda suka samu jagorancin tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung da kuma Fasto Yohana Buru na Peace Revical and Reconciliation of Nigeria dake gidansa na Kaduna a ranar Talata.

Malamin ya kwatanta yanayin rashin tsaron kasar nan da abun damuwa, inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya basu taba tsammanin hakan zata faru ba a zamanin wannan gwamnatin.

“Abinda muke tsammani daga dukkan matakan gwamnati na tarayya, jiha da karamar hukuma shine mafita ta yadda kowa zai zauna hankali kwance.

“Hatta a cikin gida zaman dar-dar ake yi, a kan titi ba a tsira ba, kuma gwamnati bata wanke mana wannan tsoron ba.

“Bamu zabesu domin mu kasance a wannan halin ba, bamu zabesu domin su siyar damu kamar dabbobi ba ko kuma su dinga mana duk yadda suka so. Abinda ke faruwa tabbas abun damuwa ne.

“Mun san gwamnati ta san abinda ke faruwa a kasar nan, mun san gwamnoninmu sun sani kuma kananan hukumomi sun sani.

“Don haka, su sauraremu saboda bama iya zuwa gona saboda tsabar tsoro. Gwamnati tayi abinda ya dace ta hanyar baiwa ‘yan kasa Musulmi da Kirista kariya daga miyagu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply