Mun Gano Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Bindiga Ke Kashe Ɗalibai – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin kaduna ƙarkashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i tayi Allah wadai da kisan wasu ɗalibai dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandire da yan bindiga keyi a jihar, tare da bada tabbacin daƙile faruwar hakan anan gaba.

A wani jawabi da kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, ya jajantawa iyalan da abun ya shafa, tare da miƙa ta’aziyar gwamnati garesu. “Wannan kisan matasan da masu garkuwa da mutanen keyi wani ɓangarene na ƙoƙarin su yaudari gwamnati.” “Kuma suna aikata wannan mummunan ta’addancin ne domin su saka gwamnatin Kaduna ta canza matsayarta daga ‘Ba biyan kudin fansa, ba tattaunawa’ zuwa yadda suke so.”

Muyiwa Adekeye ya kuma mai da martani kan wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ɗauke da wata tattaunawa da aka yi da gwamna Malam Nasiru Elrufa’i tun shekarar 2014 yana ƙalubalantar tsohon Shugaban kasa Jonathan. Inda ya yi watsi da waɗanda ke zargin gwamnan bisa matsayar da ya ɗauka a kan matsalar sace-sacen mutane a jihar.

A cikin bidiyon, Anga gwamnan jihar Kaduna na kira ga gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tayi amfani da duk wata dama, koda tattaunawa ce wajen kuɓutar da yan Matan Chibok da aka sace.

Yayin da yake kare maganar gwamnan, Adekeye yace: “Tun daga wancan lokacin da lamarin Chibok ya faru zuwa yanzun, ya nuna cewa matakin da yafi dacewa a ɗauka kan irin waɗannan sace-sacen shine ta hanyar amfani da ƙarfi, wanda hukumomin tsaron mu suke yi a halin yanzu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply