Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Nemi A Saki Wanda Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi

Wani kwamitin ƙwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su saki Mubarak Bala shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya da ake tsare da shi tsawon shekara ɗaya.

An tsare Mubarak Bala ne bayan shigar da koke ga‘yan sandan jihar Kano a arewacin kasar, kan zargin ya ci mutuncin manzon Allah a wani rubutu da ya yi a Facebook.

Ƙwararrun na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce “Kamewa da tsarewar da aka yi wa Mista Bala ba wai kawai take haƙƙin dan adam ba ne, ya yi tasiri a kan aiwatar da ƴancin walwala a Najeriya.”

Sun ce sun yi takaicin yadda hukumomi suka ki bin umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a 21 ga Disamba na sakin Mista Bala.

Kotun ta buƙaci a bayar da belinsa da kuma biyansa kuɗi 250,000 kan keta haƙƙinsa.

A ranar 20 ga Afrilu aka shirya sauraren ƙarar amma aka ɗage saboda yajin aikin ma’aikatan shari’a.

Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an mutunta dokokin shari’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply