Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Tsarin Karbar Bashin Kayayyaki Ga ‘Yan Najeriya

images 2024 03 14T070645.613

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar.

Bayanin hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar.

Tsarin zai bai wa al’umma damar inganta rayuwarsu ta hanyar samun bashin kayyaki inda za su riƙa biya sannu a hankali tsawon lokaci.

Da tsarin, jama’a na iya sayen gidaje da motoci da samun ilimi da kiwon lafiya ta hanyar bashi, inda za su biya daga baya.

Shugaba Tinubu na ganin ya kamata duk wani ɗan Najeriya ya samu damar more rayuwa ta tsarin karɓar bashi da zai taka rawa sosai wajen cimma wannan ƙudurin.

Tsarin wanda haɗin gwiwa ne tsakanin cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ƙungiyoyin tsumi da tanadi a faɗin duniya, zai faɗaɗa damarmakin mai saye na samun kaya a kan bashi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply