Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed da ke Legas.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin. Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin umarnin ƙa’idojin tafiyar da harkar sufurin jirage.
Acikin wata sanarwa da aka aikewa darakta janar na NCAA, minsitan ya ce matakin ya zamo wajibi domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin ƙa’idojin aiki musamman na matakan kariya.
Jirgin Dana ɗauke da fasinja 83 da ya taso daga Abuja zuwa Legas ya zame daga kan titinsa ranar Talata.