Tsohon Sanata, Kabiru Marafa, ya bukaci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ya janye kalamansa na bayyana kungiyar dattawan Arewa (NEF) a matsayin “Jidali” ga yankin Arewa da muranenta.
Sanata Marafa, wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, ya bukaci hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Marafa ya shawarci Matawalle wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya fito fili ya nemi gafarar dattawan yankin Arewa da daukacin ‘yan Arewa bis waɗannan kalamai na sa.
” A matsayina na dan Arewa kuma dattijo a yankin, a matsayina na mai ruwa da tsaki na jam’iyyar APC kuma wanda ya yi aiki kafada da kafada da shugaban kasa da mataimakinsa, ina so in bayyana sarai cewa wannan ra’ayi da Matawalle ya bayyana ra’ayinsa ne na kansa ba ta Shugaban kasa ko fadar Shugaban kasa ba ce, don haka a yi watsi da shi.
” Idan ba a ja wa Matawalle kunne ba, a matsayinsa na minista a gwamnatin Tinubu, za a rika ganin kamar sakon gwamnatin ya ke isarwa, kuma hakan zai iya sa farin jinin Tinubu a Arewa na raguwa natuƙa.
“Abinda na ke so a sani shine ko aso ko kar aso, waɗannan mutane dai ana kiran su dattawan Arewa ne, ci musu fuska kuma kamar an ci wa yankin da mutanen yankin mutunci ne.