Najeriya Ba Ta Yi Balagar Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ba – Baturen ‘Yan Sanda

IMG 20240227 WA0004(1)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sifeto Janar ɗin Ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai ga ta kafa ƴan sanda Jiha ba wanda gwamnoni a jihohi ke da iko da.

Egbetokun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron tattaunawa kan kafa ‘yan sandan jiha wanda kwamitin majalisar wakilai kan duba kundin tsarin mulkin kasa ya shirya.

Ya ce rundunar ƴan sandan kasa ba ta amince da hakan ba, amma kuma ta na rokon Majalisar kasa ta duba yiwuwar kara kason ƴan sanda a kasafin kuɗin kasa.

Ya kuma ce kafa ‘yan sandan jihohi zai kara ta’azzara rikicin kabilanci da ake fama da shi a Najeriya. Jawabin ya ci karo da rashin amincewar masu sauraro inda suka yi wa Okolo ihu, suna cewa ba su yarda ba.

Matsayin Sufeto Egbetokun ya sabawa matsayin da Tinubu ya bayyana a bainar jama’a game da kafa ‘yan sandan jihar.

Idan ba a manta ba, shugaba Tinubu tare da wasu gwamnonin Najeriya na bukatar a kafa ƴan sandan jihohi a Najeriya ta yadda kowacce jiha za ta rika iko da jami’sn ƴan sandan ta.

Sai dai kuma wasu da dama na ganin yin hakan zai kara ruruta kiyayya tsakanin mutanen Najeriya ganin cewa har yanzu akwai rashin yadda da juna da kuma rikice rikice na addini da na kabilanci da ya ki ci yaki cinye wa

Labarai Makamanta

Leave a Reply