Dakarun sojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi da ƙungiyar masu tayar da kayar-baya ta ISWAP ke amfani da shi a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.
A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ƙungiyoyin ta’addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce haɗin gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF ne suka gano wurin gasa burodin yayin wani samame da suka kai maɓoyar ƴan ta’addan ranar Lahadi.
“Majiyoyi sun ce an lalata gidan burodin tare da ƙwato kayayyaki da suka kunshi manyan injunan bayar da hasken wutar lantarki guda biyu, wani abin gasa burodi da kuma wasu kayan haɗi da ake yin burodi da dama,” kamar yadda Makama ya ruwaito.
A cewar rahoton, gano wurin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka kai wani samame na tsawon mako ɗaya da zimmar kakkaɓe ƴan ta’dda daga yankunan da suka fi karfi a dajin Timbuktu Triangle, da sauran yankuna da suka haɗa da Talala, Ajigin, Dusula, Abulam da kuma Gorgi – waɗanda suka kasance wurare masu haɗari da ƙungiyoyi masu tsattsaurar ra’ayi ke zama.
“Waɗannan ƙungiyoyin ƴan ta’dda yawanci su ke da alhakin kai hare-hare, kwantan-ɓauna, binne abubuwan fashewa a kan hanyoyin Damboa, da Damaturu-Maiduguri, kai hare-hare garuruwan Askira, Buratai, Buni Yadi, da kuma lalata layukan wutar lantarki da ke haɗa Borno da Yoba,” in ji Makama.
Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da aikin fatattakar ƴan ta’ddan babu kakkautawa, duk da irin haɗari da wasu yankuna ke da shi, musamman ganin sansanonin ƴan ta’addan na cikin manyan dazuka da kuma binne abubuwan fashewa da suke yi kan hanyoyi da za su kai wurinsu.