Matainakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed tace hanyar da za’a bi wajen yaki da ayyukan ta’addanci itace ta tabbatar da adalci a tsakanin jama’a da kuma jagoranci na gari.
Mohammed ta yi kiran mayar da hankali a kan illar da ayyukan ta’addanci ke yiwa ‘yan mata da mata tare da matasa, inda ta bukaci taimakawa wadanda ta’addanci ya shafa.
Amina Mohammed ta sanar da hakan ne a yayin taron lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro dake addabar Najeriya musamman yankin arewacin kasar da ya gudana a ƙasar Amurka.
Gwamnonin Jihohin Arewa inda ke fama da matsalar tsaro duk sun halarci wannan taro da majalisar dinkin duniya ta shirya domin kawo karshe rikicin ta’addanci wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Najeriya.