Mun Ci Gajiyar Rufe Boda – Manoman Najeriya

Yayin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ƙoƙarin miƙa mulki bayan shekara takwas, shin wane tasiri manufofinta suka yi kan harkar noma?

BBC ta tattauna da shugabannin wasu ƙungiyoyin manoma a Najeriyar waɗanda suka bayyana yadda harkar noma ta kasance a tsawon mulkin shugaban mai barin gado.

Akasarin manoman sun yaba wa gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari, waɗanda suka ce harkar noma ta inganta ta hanyar taimaka masu tsayawa da ƙafafunsu.

Manoman sun ce a cikin shekara takwas na gwamnatin Muhammadu Buhari, shugaban ya ɓullo da shirye-shirye wadanda suka amfanar da su tare da samar da wadataccen abinci da ake amfani da shi a ƙasar.

Ɗaya daga cikin matakan da Buhari ya ɗauka shi ne garƙame iyakokin ƙasar ta ƙasa inda aka hana shiga da shinkafa yar waje cikin Najeriya.

Shugaban ƙungiyar manoma ta NICAS, Sadiq Daware ya ce manoma sun ci gajiyar gwamnati da za ta tafi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply