Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Majalisa

Rahotanni daga zauren Majalisar Dattawa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin kula da kudaden gwamnati na Majalisar ya bayyana cewa sakamakon binciken da ya gudanar ya gano cewa ma’aikatan gwamnati sun fi aikata cin hanci da rashawa idan aka kwatanta da ‘yan siyasar kasar nan.

Shugaban kwamitin Sanata Matthew Urhoghide, shi ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da yayi da manema labarai a Abuja.

Kwamitin wanda shi ne kadai kwamitin Majalisar Dattawa da tsarin mulki ya yi na’am da shi, a halin yanzu yana kan aikin kalailaice rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya na 2015 zuwa 2018.

Rahoton Mai Binciken Kudin Tarayyar ya kunshi binciken da ya gudanar kan asusun ajiyar ma’aikatu da cibiyoyin da kuma kafofin gwamnatin tarayya.

Sanata Urhoghide ya koka cewa sakamakon Binciken Kwamitin ya gano mafi munin cin hanci da rashawa wanda ya yi wa lakabi da suna ‘cin hanci da rashawan cibiyoyi’ yana faruwa ne a bangaren aikin gwamnati.

“Bari in bayyana wannan abin, muna a lokacin da ake gaggawar yin zarge-zarge, inda mutane suke hanzarin tsinuwa musamman a kan ‘yan siyasa. “Kowa ya yi imanin cewa duk wata aika-aika a kasar nan ‘yan siyasa ne ummul haba’isinta, amma za mu ci gaba da fada musu cewa idan ka tattara dukkanin jam’iyyun siyasar kasar nan da daukacin mambobinsu, ba su kai kashi 10 na al’ummar Najeriya ba.

Don haka ba ba mune da rinjaye a kasar nan ba. “Abin da kwamitinmu ya gano shi ne sace kudin gwamnatin da ake yi ba ‘yan siyasa ne ke satar su ba. “Mun gano biliyoyin nairar da aka sace daga cikin asusun ma’aikatu da kafofin gwamnati.

“Dan Allah, ‘yan siyasa nawa ne suke da wadannan makudan kudaden? Ya ce suna gayyatar jagororin ma’aikatu wadanda su ma’aikatan gwamnati ne domin su yi musu bayanin kudaden da aka sace. Mun gano biliyoyin naira da aka kashe ba tare da wata kwakkwarar hujjar da doka ta ta bada ba, a cewarsa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply