Kano: Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kama Mawakin Da Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi

Hukumar Tace finafinai da dabi’i ta jihar Kano tare da hukumar tsaro na farin kaya DSS reshen jihar Kano sun sami nasarar damke wani matashi mai suna Ahmad Abdallah wanda ya yi wakar ‘batanci ga jabanin Ubangiji.

Matashi Ahmad wanda d’an uwan mawaki Hafiz Abdallah ne, an zarge shi da wuce gona da iri da kuma furta kalamai a cikin wakar da ya saki mai taken ‘GWASKA BARHAMA MAGANIN BALA’I’ Wanda ya furta kalamai ga Shehi Ibrahim Inyass, kalaman da ake furta su ga Ubangiji kadai ba wani ba.

Saboda irin wannan, ya sa gwamnatin Kano karkashin hukumar ta tace Finafinai ta dabbaka dokar tace wakokin yabo kafin a sake su gudun faruwar wuce gona da iri da hukumar ta zargi matashin da aikatawa wanda ya bijire umarnin hukumar ta hanyar sakin wakar ba tare da an tace ba.

Malam Ismail Naabba Afakallahu shugaban hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano ya jaddada cewa hukuma ba za ta zuba ido ta kyale ana taba hurumin Ubangiji a Kano ba.

” Saboda kula jabinin Allah a cikin kasida, da janibin Manzon Allah (S.A.W) da kuma su kansu bayin Allah Shehinnai wadanda ake samun tarbiyyar kusanci da Allah ta wajensu. Don haka duk wanda ya saki kasida ba tare da an tace ba, muna tabbatar masa cewa ya hadiyi tabarya, ba shi ba kwanciya ba zama, dole hukuma ta yi aiki a kansa ta hanyar ladabtarwa, hakan ya zama horo a kansa da kuma darasi da izina ga wanda ya ke son ya aikatawa.” In ji Malam Afakallahu.

Ya bayyana cewa dauri ko kamu ba burin hukuma ba ne. Abin da hukuma ta ke yi shi ne kokarin kawo gyara da tsaftacewa don a gudu tare a tsira tare.

Labarai Makamanta

Leave a Reply