Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Zanga-zangar Rashin Tsaro A Arewa

Uwargidan Shugaban ƙasa Aisha Buhari ta bi sahun masu kira a kawo ƙarshen rashin tsaron da ke addabar Arewacin Najeriya.

Uwargidan shugaban kasar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter ranar Asabar tare da wakar mawakin Kannywood, Adam A. Zango inda yake kokawa kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriya.

Sakon nata na ɗauke da maudu’in #Achechijamaa, wanda ke nufin a ceci rayuwar jama’a. Wakar na ɗauke da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar da ke nuna su a fadar shugaban ƙasa suna ganawa.

Wasu daga cikin baitukan wakar na cewa:

“Don Allah a duba,

Taimakonka [Shugaba Buhari] muke nema

Arewa na kukaye,

Ana zubar da jininmu

Ana kashe al’umarmu

Ana ƙona dukiyarmu…

Masu amshin suna kiran sunan Baba, wato Shugaba Buhari.

Mai dakin shugaban kasar ta wallafa saƙon ne a yayin da ‘yan Najeriya, musamman daga kudancin ƙasar ke tsaka da zanga-zanga kan gallazawar da rundunar ‘yan sandan ƙasar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS, wadda aka rusa, take yi musu.

Suna amfani da maudu’in #EndSars don jawo hankali kan wannan matsala da ma wasu matsalolin da ke addabarsu.

Kazalika takwarorinsu na arewacin kasar suna tasu zanga-zangar kan taɓarɓarewar tsaro a yankin inda suke amfani da mau’du’in #SecureNorth don bayyana halin da yankin ke ciki.

Ɗaruruwan mutane ne suka mutu yayin da dubbai suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar a shekarun baya bayan nan.

Hakan na faruwa ne a yayin da yankin ke ci gaba da fama da hare-haren mayaƙan Boko Haram waɗanda aka kwashe shekara da shekaru ana fuskanta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply