Labarin dake shigo mana yanzu haka daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Malaman jami’o’in gwamnati a duk fadin kasar suna barazanar sake shiga wani sabon yajin aiki.
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi wannan barazanar ne a lokacin da ta zargi babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da kin biyan albashi da kuma fitar da kudaden alawus na sama da ma’aikata 1000 na tsawon watanni 13, kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya.
Lazarus Maigoro, shugaban ASUU na jami’ar Jos, ya yi wannan barazanar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato.
Ƙungiyar ta zargi babban akanta da rura wutar rikici tsakanin gwamnatin tarayya da Kungiyar malaman ta Jami’o’i.
“Duk da umarnin da shugaban kasar ya bayar na biyan albashin dukkan malaman jami’ar, Akanta Janar ɗin ya ki biyan albashinsu da suka fara daga watanni hudu zuwa 13.
“Babban abin damuwa shi ne yayin da Babban Akawun ke kin biyan wadannan albashin, ma’aikatansa a cikin OAGF sun dukufa wajen kiran malaman da abin ya shafa da kuma dagewa kan cewa sai sun yi rajista da IPPIS kafin a biya su; wasu ma ana neman su hakura da wani bangare na albashinsu domin a biya su. Don haka a fili yake cewa wannan wani aiki ne da gangan daga ɓangaren AGF da mukarrabansa wanda ba za’a lamunta ba”