Kafa Kwamitin Bincikar El-Rufa’i Babban Darasi Ne Ga ‘Yan Siyasa – Aisha Yesufu

IMG 20240420 WA0019

Fitacciyar ‘yar fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu ta yi shaguɓe ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da na Kogi, Yahaya Bello. Aisha ta yi hakan ne yayin da tsoffin gwamnonin ke cikin mawuyacin hali bayan kammala wa’adinsu a matsayin gwamnoni.

Yesufu ta bayyana haka ne a shafinta na X inda ta ce ‘yan siyasar Najeriya sun dauka shekaru takwas za su tabbata.

Ta ja kunnen ‘yan siyasar Najeriya da su mayar da hankali yayin da suke kan madafun iko. “A wurin ‘yan siyasar Najeriya, shekaru takwas za su tabbata, abin da basu sani ba kenan.” “Ina dariyar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello.” – Aisha Yesufu

Labarai Makamanta

Leave a Reply