Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai ci gaba da kare ha??in musulmi a fa?in duniya.
Shugaban ya fa?i haka ne cikin wata sanarwa mai ?unshe da sa?on fatan alheri ga al’ummar musulmi yayin da suka soma azumin watan Ramadan a ranar Talata.
Shugaban ya ce yana alfahari da ya ?age haramta wa wasu ?asashen musulmi shiga Amurka.
“Zan ci gaba da tsayawa kan kare ha??in ?an adam a ko ina, har da ?an ?abilar Uyghur a China da rohingya a Burma da kuma dukkanin musulmi a fa?in duniya.
Ya kuma ce dole a kawo ?arshen barazana da ?yama da ake nuna wa musulmi a Amurka, a cewarsa: “babu wani a Amurka da zai kasance cikin fargaba don bayyana addininsa.”
A nasa ?angaren sakataren harakokin wajen Amurka Antonu J. Blinken bayan ya yi wa musulmi murnar Ramadan ya kuma ce Amurka za ta ci gaba da inganta hul?a da ?asashen musulmi.