Badakalar Yahaya Bello: Babban Lauya Ya Yi Kiran A Yi Gaggawar Tsige Gwamnan Kogi

IMG 20240420 WA0018

Yayin da ake ci gaba da neman tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Gwamna Usman Ododo ya sake shiga matsala. Wani fitaccen lauya a Najeriya, Deji Ajare ya bukaci Majalisar jihar Kogi ta tsige Gwamna Ododo kan hawan ƙawara ga dokokin kasa.

Ajare ya ce abin da gwamnan ya aikata na tserewa da Yahaya Bello ya saba dokar kasa wanda ya cancanci hukunci, kamar yadda ya wallafa a shafin Facebook.

Ya bukaci kakakin Majalisar, Umar Yusuf da ya fara shirin tsige gwamnan da gaggawa saboda neman maslaha kan abin da ya aikata.

Wannanna kunshe ne a cikin wata takarda da lauyan ya tura ta hannun magatakardan Majalisar a ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu.

Ya bayyana laifuffukan da Ododo ya aikata Ya ce sulalewa da gwamnan ya yi da mai gidansa ya aikata babban laifi na kawo cikas ga shari’a da kuma boye mai laifi. Har ila yau, lauyan ya bukaci Majalisa da ta haɗa kai da hukumar EFCC domin tabbatar da dukkan masu laifin sun gurfana domin amsa tambayoyi.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Ododo ya tsere da mai gidansa, Yahaya Bello a idon jami’an hukumar EFCC.

Labarai Makamanta

Leave a Reply