Hajjin Bana: Babu Maniyyacin Da Zai Saura A Najeriya – Hukumar Alhazzai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar alhazai ta ƙasa ta jaddada cewa tana da ƙwarin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage a ƙasa yayin da ake shirin rufe jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a daren ranar Lahadi.

Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na alhazan Najeriya.

Daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu ƙarin awanni na ci gaba da aikin.

Yayin wani taron manema labarai a Abuja NAHCON ta ce tana da ƙwarin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply