Rashin Gaskiya: Buhari Ya Kori Sabon Akanta Janar

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta cire mukaddashin babban akanta Janar Mr. Chukwuyere N. Anamekwe inda aka maye gurbinsa da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, wanda tsohon darekta ne a tsarin asusun gwamnati na bai-daya, wato, TSA (Treasury Single Account).

Rahotanni na cewa an maye gurbin mai rikon mukamin na Akanta-Janar din ne saboda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, na bincike a kansa.

Haka kuwa ana cewa gwamnatiun ba ta ji dadin wasu kalamai da ya yi ba inda ya ce, Najeriya na ranto kudi domin ta biya albashi.

Anamekwe wanda aka nada shi a wannan matsayi na rikon-kwarya a ranar 22 ga watan Mayu bayan da hukumar EFCC ta kama Babban Akantan kasar, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da naira biliyan 80, ya yi kalaman cin bashin ne, a ranar 14 ga watan Yuni, na 2022, kuma kwana bakwai daga nan aka cire shi.

Mista. Sylva, wanda ke zaman mukaddashin Babban Akantan a yanzu, rahotanni na nuni da cewa zai yi ritaya a cikin watanni uku na farkon shekara mai zuwa, 2023.

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriyar ta kaddamar da neman wanda za ta nada a matsayin sabon Babban Akantan, kamar yadda bayanai ke nunawa.

Jaridar The Nation ta Najeriyar ta ruwaito cewa duk wani kokari da ta yi na neman gaskiyar kalaman da Anamekwe ya yi cewa gwamnati na ciyo bashi ta biya albashi, ya ci tura.

Labarai Makamanta

Leave a Reply