Raina Fansa Ne Ga ‘Yan Najeriya – Hamza Al-Mustapha

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha ya jaddada kudirinsa na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.

Al-Mustapha, wanda shine dan takarar shugaban ?asa na jam’iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke “ya sadaukar da rayuwarsa don Najeriya da walwalar yan Najeriya”.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a yayin hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.

“Wannan karon na amsa kiran yan Najeriya da dama, manya da yara daga Arewa zuwa Kudu da kungiyoyi da dama. Kiran ya zo ne daf da lokacin mika fom din takara ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta”.

“Mun zauna mun kalli wasu jam’iyyun, mun zabi wanda akidunmu suka zo daya muka gano Action Alliance na da abin da muke bukata. Mun shiga Action Alliance kuma muna ta aiki ta karkashin kasa tun bayan gangamin taro.

Al-Mustapha ya ce fatansa shine ya zama shugaban Najeriya kuma ayyukan da ya yi a baya sun isa zama hujja a kansa. “Na yi aiki a wurare da dama kafin in zama soja. Na yi abin da ba za ka iya fahimta ba cikin gaggawa, musamman yi wa Najeriya hidima. Abin da muka yi a soja hujja ne.”

Related posts

Leave a Comment