Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar alhazai ta ?asa ta jaddada cewa tana da ?warin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage a ?asa yayin da ake shirin rufe jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a daren ranar Lahadi.
Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na alhazan Najeriya.
Daga ?arfe 12:00 na daren ranar Lahadi wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu ?arin awanni na ci gaba da aikin.
Yayin wani taron manema labarai a Abuja NAHCON ta ce tana da ?warin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa ?asa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.