Gwamnatin Tinubu: Na Fi Karfin Mukamin Ministan Abuja – El-Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa ba zai riƙa zuwa Kaduna ba har sai in ya zama dole bayan kammala wa’adin mulkinsa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Abuja, a wajen taron ƙaddamar da wani littafi a ranar Talata. El-Rufai’n ya ce ba zai amshi kujerar Ministan Birnin Tarayya ba koda an bashi.

Sai dai gwamnan bai bayyana cewa ko zai zamo ɗaya daga cikin waɗanda za a tafi da su a wannan gwamnati ko a’a ba, illa iyaka dai ya bayyana cewa ba zai karɓi kujerar ministan Abuja ba.

El-Rufai dai ya kasance shine tsohon ministan Abuja a lokacin tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, wanda a lokacinsa an yi gagaruman ayyuka, ciki kuwa hadda rushe-rushen manyan gurare a Abuja.

“Na gama aiki na, na gama, bana waigawa baya. Tun da na bar birnin tarayya ban ƙara komawa ba sai a shekarar 2016, lokacin da aka bawa wani ɗan ajinmu a sakandire muƙamin minista.” “Duk wani muƙami da na bari, ba na sake waiwayar shi, idan na bar Kaduna nan da kwanaki 19, ba zan riƙa ma zuwa ba sai in ya zama dole.”

El-Rufai ya ƙara da cewa: “Koda an bani muƙamin, to ba zan karɓa ba in tafi Abuja ba. Kamar yadda nace, ba na maimaita aji, kuma nasan matasa masu ɗanyan jini da zan iya turowa su yi aikin fiye da yadda na yi a lokacin ina ministan.” “Shekaru na sun yi ma muƙamin yawa. Yanzu na girmi yin rusau, a samu matashi mai jini a jika ko matashiya a bata muƙamin.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply