Yayin da Najeriya ke fama da kalubalen tsaro ta bangarori da dama, garkuwa da mutane ya zame masana’antar kasa baki daya ya kuma zama dabarar da aka fi so ta kungiyoyin ‘yan fashi da masu jihadi.
Harin na baya-baya da aka kai a makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna ya biyo bayan sace mutane da aka yi a yankin arewa maso gabas a makon jiya, inda aka ce sama da mutane 100 sun bace.
Menene asalin?
A farkon shekarun 2000, masu garkuwa da mutane sun kai hari kan ma’aikatan mai a yankin Neja Delta, amma lamarin ya kara ta’azzara karkashin yan kungiyar Boko Haram a shekarar 2009 a yankin arewa maso gabas.
Har yanzu dai kungiyar Boko Haram da kungiyar IS da ke yammacin Afirka na ci gaba da yin garkuwa da wasu mutane.
Mayakan da ke yakar masu da’awar jihadi sun zargi ISWAP da yin garkuwa da jama’a a Ngala, jihar Borno a makon da ya gabata, wanda ya addabi mata da kananan yara daga sansanonin wadanda rikicin yankin arewa maso gabas ya raba da muhallansu.
A baya dai kungiyoyin sun kai hari kan makarantu da manyan makarantu, sai dai a baya-bayan nan an dan samu ja baya a irin wadannan hare-hare.
Kungiyoyin masu garkuwa da mutane kuma suna gudanar da ayyukansu a duk fadin kasar, inda suke bin kowa daga ’yan makaranta zuwa iyalan sarakunan gargajiya.
Wasu masana dai na ganin matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasar a yanzu ce ke janyo karuwar sace-sacen mutane a yayin da ‘yan Najeriyar da ke cikin halin kaka-ni-kayi ke komawa aikata laifuka domin samun kudin shiga.
Wata cibiyar bincike mai suna SBM a Najeriya ta ce ta samu rahoton mutane 4,777 da aka sace tun lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
Sace ‘yan matan makarantar Chibok 276 da mayakan Boko Haram suka yi a arewa maso gabashin Najeriya ya dauki hankula a duniya shekaru goma da suka gabata.