Shugabancin Majalisa: Fusatattun Sanatoci Sun Yi Watsi Da Rabon Mukamai

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabanin ƙaddamar da majalisar dokoki ta 10 a watan Yuni, fusatattun zaɓaɓɓun sanatoci daga APC sun gana da mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar mai mulkin Najeriya a hedkwatarta da ke Abuja.

Daga cikin sanatocin da suka halarci taron, akwai Abdulaziz Yari da Orji Kalu da Mohammed Musa da kuma Sadiq Umar.

Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Iyiola Omisore da shugabar mata ta APC Beta Edu, su ma sun halarci taron.

Da yake jawabi ga kwamitin, Orji Kalu wanda ke neman takarar shugaban majalisar dattawa ya ce bai wa kowanne ɓangaren Najeriya dama abu ne mai kyau.

Ya ƙara da cewa, bai kamata jam’iyyar ta miƙa shugabancin majalisar da ba a kai ga ƙaddamar da ita ba, bisa dalilai na yawan ƙuri’un da kowanne yanki ya bayar wajen samun nasarar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ba.

A cewarsa, shiyyar da ƙuri’unta ba su taka kara sun karya ba a zaɓen da ya gabata, na iya samar da ƙuri’u masu yawa ga jam’iyyar a zaɓuka masu zuwa.

Shi ma Yari, wanda ya gabatar da takardar adawa da zaɓaɓɓun sanatocin suka rubuta ga Shugaban APC, ya nemi jam’iyyar ta sake nazari kan tsarin da ta amince da shi saboda adalci da daidaito.

A ranar Litinin ne kwamitin gudanarwar APC ya raba muƙaman shugabannin majalisar tarayya ta goma.

APC ta miƙa shugabancin majalisar dattawa ga Sanata Godswill Akpabio (shiyyar kudu maso kudu) sai muƙamin mataimakin shugaban majalisar ga Sanata Barau Jibrin (shiyyar arewa maso yamma).

Sai kuma muƙamin kakakin majalisar wakilai ga Abass Tajudeen (Arewa maso Yamma), muƙamin mataimakin kakakin ga Ben Kalu (yankin Kudu maso gabas).

Labarai Makamanta

Leave a Reply